Yanzu-yanzu: Tinubu ya yiwa yan wasan Super Eagles Alkawari gwagwgwabar kyauta

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shugaban Nigeria Bola Tinubu yayi alkawarin bada lambar yabo ga yan wasan Kwallon kafa na super eagles da suka buga wasa a AFCON 2024.

 

Hakan na cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan shafukan sada zumunta Olusegun Dada a shafin sa na X a ranar Talata.

Wata Kungiya Ta ce Zata Maka Gwamnan Kano a Kotu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa dukkan membobin kungiyar Kwallon kafa ya Najeriya lambar yabo ta member na Order of Niger (MON),” kamar yadda tweet din ya karanta.

Yan Hisbah a Kano Sun Kama Tauraruwar TIKTOK

Ya kara da cewa, Tinubu ya yabawa ‘yan wasan da daukacin yarin Nigeria da suka halarci wasan cin kofin zakaran Kasashen Africa, bisa jajircewar da suka yi da kuma daga darajar al’ummar kasar a gasar AFCON da aka kammala kwanan nan,

” Duk da cewa ba mu ji dadin rashin nasarar da da bamu samu ba, amma Super Eagles sun nuna bajintar wasanni kuma sun yi iya bakin kokarin su”.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Lahadi Kasar Ivory Coast ta Lallasa Nigeria da ci 2 da 1 a wasan karshen da Cin kofin zakaran Kasashen Africa wato AFCON 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...