Yan Hisbah a Kano Sun Kama Tauraruwar TIKTOK

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Hukumar Hisbah ta jihar Kano tace ta sami nasarar kama shahararriyar jarumar TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya.

Hukumar Hisbah ce da kanta ta tabbatar da hakan, Inda tace sun kama Murja Kunya ne sakamakon ci gaba da tayi da yin abubuwan rashin da’a , da suka sabawa koyarwar addinin Musulinci.

Sarkin Kano ya Baiwa Matar Tinubu Sako Zuwa ga Shugaban Kasa

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito, a baya hukumar ta gayyaci murja da sauran Taurarin TikTok don yi mata nasiha tare da lura da irin abubuwan da ta ke aikata a shafukan sada zumunta sai dai ba ta sauya wa, hakan ne ya sanya hukumar kama ta.

Tsadar Rayuwa A Najeriya Ba Laifin Tinubu bane, Ina da Dalili –Khalifa Sanusi II

Jarumar Tiktok din dai ta shahara, wajen furta kalaman batsa da rashin tarbiya da kuma sanya sutura da ta saba wa addinin musulinci da al’adar Hausawa tare da kwaikwayon wasu al’adu na daban.

Tun a baya dai jama’a da dama ke ganin baikon hukumar Hisbar na kin kama Murja Kunya sakamakon yadda ta shafa wa idon ta da toka, ta ke shuka rashin mutunci a shafukan sada zumunta, iya son ranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...