Zanga-zanga ta barke a Jihar Sokoto kan tsadar rayuwa

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Mazauna Sokoto a ranar Litinin sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.

Majiyar KADAURA24 ta PREMIUM TIMES ta gano cewa masu zanga-zangar sun yi tattaki ne daga unguwar Tudun Wada da ke babban birnin jihar zuwa kofar gidan gwamnati.

Tsadar Rayuwa A Najeriya Ba Laifin Tinubu bane, Ina da Dalili –Khalifa Sanusi II

Wasu daga cikin masu zanga-zangar suna rike da alluna, suna rera waken “Wake tsada”, “Masara tsada” “Man fetur yltsada” da sauransu.

‘Yan Najeriya na kokawa da hauhawar farashin kayayyaki da kuma taɓarbarewar tattalin arziki da ya ta’azzara sakamakon cire tallafin man fetur a watan Mayun bara.

Farashin kayayyakin abinci da sauran kayayyakin masarufi sun yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya janyo tabarbarewar tattalin arzikin kasar da tuni ya yi kasa a gwiwa.

Sarkin Kano ya Baiwa Matar Tinubu Sako Zuwa ga Shugaban Kasa

An yi irin wannan zanga-zanga a jihohin Neja da Kano a makon jiya yayin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC suka bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni biyu da ta fara aiwatar da tsare-tsaren da za su rage wa ‘yan Najeriya radadin talauci.

Da yake jawabi ga manema labarai, Abdullahi Muhammad, wanda ya jagoranci zanga-zangar, ya ce lamarin ya sa jama’a sun kai bango yanzu.

“Abin mamaki ne yadda babu wanda ke kokarin rage farashin kayan masarufi, mun zabi wadannan mutane ne da fatan al’amura za su gyaru amma al’amura suna kara tabarbarewa, muna bukatar a duba farashin domin tabbatar da daidaiton farashin kayayyaki,” inji shi.

Ya kuma zargi ‘yan kasuwa da tara kayayyaki da kuma kara farashin kayayyakin ba dole ba, yana mai kira ga gwamnati da ta kara himma wajen sa ido kan harkokin kasuwanci.

Muduwar garin Garri Naira 1,250 ne, yayin da mudu na garin masara ya kai Naira 1,700, ‘yan kasuwa na cikin matsalar domin sune ke kara farashi yadda suke so,”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...