Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Ministan yaɗa labarai a Najeriya, Idris Malagi ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hannu a rikicin siyasar da ake yi a jihar Rivers.
Ministan ya yi magana ne a gidan Talabijin na Channels yau Alhamis inda ya ce kasancewar wasu da ke cikin rikicin na cikin majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu, hakan ba wai yana nufin gwamnatin APC ce ta kitsa halin da ake ciki ba a jihar.
“Ban gano wata shaida da zan iya cewa gwamnatin tarayya ce take ingiza rikici a jihar Rivers ba,” in ji ministan.
Mun kashe sama da Naira Miliyan 160 Wajen gyara makarantar G.G.C Dala – Shugabar kungiyar DOGAA
Ya ƙara da cewa abu ne mai sauki a yaɗa jita-jita saboda wasu da ke cikin rikicin mutane ne da suke da kusanci da gwamnati”.
Malagi ya bayyana cewa akwai rikicin siyasa a wasu jihohin kamar Ondo kuma Shugaban ya sa baki aka warware rikicin da ya shafi ƴan jam’iyya daya.