Daga Aisha Aliyu Umar
Kungiyar dake yaki da cin zarafin Mata da Yara ta jahar Kano ta ba zata saurara ba wajen cigaba da yaƙi da cin zarafin ‘ya’ya mata a fadin jihar.
Shugabar kungiyar Hajiya Gambo Abdullahi ta bayyana hakan ne yayin wani taron kin jinin cin zarafin ‘ya’ya mata da Yara kanana a Kano.
” Cin zarafin ‘ya’ya mata na kara yawa a kano don haka dole mu tashi tsaye don ganin mun yaki wannan harkar, don haka muna bukatar hadin kan dukkanin masu ruwa da tsaki don ganin mun kau da wannan mummunar dabi’ar a cikin al’ummar mu”. A cewar Hajiya Gambo

“Ina baiwa iyaye shawarar su kara zage dantse wajen ganin sun kyautata rayuwar ya’yansu, musamman ma masu tura ya’yan su aikatau, saboda ana azabtar da su kuma hakan cin zarafi ne, ya kamata iyaye su sani cewa hukuma ba zata saurarawa duk wanda aka kama da cin zarafin ‘ya’ya mata ko kananan yara”.
Ta mu Kara da cewa “samari masu yaudarar yara mata da abun hannun su shi ma cin zarafi ne, wani lokacin ma a cikin gida ake bata yaran kuma zamu dauki dukkanin matakan da suka dace wajen tabbatar da an hukunta duk wanda aka kama da hannu wajen lalata rayuwar yara”.
Da dumi-dumi: Gwamnatin Tinubu ta bayyana matsayarta kan rikicin siyasar Rivers
Ta kuma tabbatar da cewar Kungiyar su ba zata zuba Ido tana kallon wannan mummunar dabi’a ta bata ya’ya mata na kara ta’azzara a cikin al’umma ba.
Dr. Hajiya Hadiza Gishiri wace Uwace A wannan Qunqiyar tana kira ga iyaye Mata da suji tsoron Allah su kula da yayansu musamman masu kai ya’yan su aikatau Inda ta ce ” suma fa ya’ya ne kamar kowa” ta Kuma yi addu’a Allah ya Basu sa’a a Wannan tafiyar tasu.
Taron dai Yasami Halartar Gungiyoyin Mata daban daban Da kuma Maza Da Yan Jaridu Ciki Harda Tsofafin Sojoji.