Abubawan da muka tattauna da masu gabatar da Shirin “Mata a Yau” na Arewa24 – Sheikh Aminu Daurawa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shehun malamin nan Kuma babban Kwamandan hukumar Hisbah ta jihar kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi bayanin dalla-dalla kan yadda suka yi da matan nan dake gabatar da shirin Mata A Yau na tashar talabijin ta Arewa24.

 

” Matan nan sun zo hukumar Hisbah cikin tashin hankali sun ce min ma kusan kwana daya kenan ko abinci sun kasa ci, dayar ma ta ce min bata karya ba nace ai ga abinchin an kawo min ko na bata taci, saboda tausayi da ganin irin damuwar da suka shiga sosai”.

 

Sheikh Daurawa ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da gidan Radio Freedom dake Kano.

Talla

Yace sun fadamin cewa sun ji Malamai suna ta zagin su suna la’antarsu, kuma ba wani malami da ya kirawo su domin jin ta bakinsu, saboda su Musulmi ne kuma sun musanta cewa suna kokarin kawo auren jinsi da batun kokarin zuga mata da ake cewa suna yi.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya maka gwamnatin kano da wata hukuma a gaban kotu

” Sun faɗa min cewa ba dukansu ne zawarawa ba, akwai mai aure a cikin su akwai wacce kuma ta kusa yin auren akwai Kuma wacce uwace kakace a wajen kusan duk malaman da sukai magana tunda tace aurenta na farko an yi mata a Shekarar 1979″. A cewar Kwamandan Hisbah

Sheikh Daurawa yace tunda matan sun yarda sun yi kuskure ya ɗauki gabarar kiran malaman da suka yi maganganu akan batun don fahimtar da su , Inda yace nan take ya kirawo Dr. Abdullah Gadon kaya Inda ya sanar da shi halin da ake ciki shi ne suka ce Shima zasu ziyarce shi domin su yi masa bayani.

Hotunan yadda Sabon Shatale-talen Kofar Gidan Gwamnatin Kano ya kasance

Sheikh Daurawa yace da su”Ku kwantar da hankalinku zamu dauki duk wasu matakai da suka dace domin fahimtar da malaman , sannan Kuma ku rika tuntubar Malamai akan abun da ya shafi addinin musulunci, sannan ku cigaba da baiwa mata shawarwarin da zasu kara inganta zaman aure .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...