Hakikanin Abun da ya faru a Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano a zamanta na ƙarshe

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta dage hukuncin karar da jam’iyyar APC ta shigar na kalubalantar nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP .

 

Shugaban tawagar alkalan mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, wanda ya yi alkawari a madadin sauran alkalan na yin adalci ga dukkan bangarorin, ya ce hukuncin zai zo ne kafin kwanaki 180 da doka ta ba su.

 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa jam’iyyar APC na kalubalantar INEC kan ayyana Kabir-Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

 

Wadanda suka akai karar sun hada da: INEC, Kabir-Yusuf, da kuma NNPP .

Talla

Kwamitin mai mutane uku karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, ya ce kotun za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci bayan dukkan bangarorin sun amince da rubutaccen bayaninsu na karshe.

“Ina farin ciki cewa wannan shi ne aikina na farko a matsayina na Shugaban Kotun Sauraren kararrakin zabe kuma na yi addu’ar Allah ya yi mini jagora wajen tabbatar da adalci a aikina.

Kawu Sumaila ya ɗauki nauyin Karatun dalibai 100 a Kano ta Kudu

“Za mu yi adalci. Ku tabbata cewa za mu karanta abin da doka ta ce kuma za mu karanta shi gwargwadon iliminmu,” in ji Akintan-Osadebay.

Tun da farko, Lauyan jam’iyyar APC, Offiong Offiong SAN, a lokacin da ya amince da rubutaccen bayaninsu na karshe a ranar 31 ga watan Yuli, 6 ga watan Agusta, 7 ga watan Agusta, da kuma Agusta 8, ya mayar da martani kan batutuwan da suka shafi doka.

Da dumi-dumi: NNPP Ta Maka Kwankwaso Kotu Bisa Zargin yiwa jam’iyyar Zagon Kasa

“Muna kira ga kotu da ta dauki bayaninmu da aka rubuta a matsayin hujjar mu sannan kuma muna rokon kotun da ta tabbatar da kokenmu ta kuma ba mu narar da muke fata.

“Mai kara na biyu ya kawo rajistar zama mamban jam’iyyarsa har sau biyu kafin zabe da kuma bayan zabe.

“Ya nuna cewa wanda ake kara na biyu ba dan jam’iyyar NNPP ba ne kafin zabe, ya zama mamban jam’iyyar ne bayan zaben.

“Duk takardun zabe da aka yi amfani da su a wasu kananan hukumomi ba a sanya hannu, tambari da kwanan wata ba”

Shima a nasa bayanin, Lauyan Hukumar INEC, Emmanuel Osayomi yace ya shigar da rubutaccen bayaninsu mai kwanan watan Aug.1 sannan ya shigar da Aug.2.

Osayomi ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar saboda wanda ya shigar da wadanda suka Shigar da karar basu da isassun hujjoji kan karar .

Lauyan Kabir-Yusuf, Adegboyega Awomolo, SAN, ya shigar da bayaninsu na ƙarshe a rubuce a ranar 31 ga watan Yuli kuma ya shigar da karar a ranar 1 ga Agusta.

“Ina roƙon Mai Shari’a da ya yi watsi shaida na 31 wato Pw31 wanda yayi a ranar 26 ga Mayu, babu wata shaida,” in ji Awomolo.

Dage zaman dai ya biyo bayan jawabin karshe da jam’iyyar APC ta yi da ta bukaci kotun da ta tabbatar da karar da kuma mayar da Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben yayin da INEC, NNPP da Yusuf suka bukaci kotun da ta yi watsi da karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...