Daga Abdulrashid B Imam
An zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, da yiwa jam’iyyar zagon kasa a zaben da ya gabata.
Gamayyar shugabannin jam’iyyar na jihohi ne suka yi wannan zargin.

Shugabannin jam’iyyar NNPP na jihohi ne sun yi ikirarin cewa Kwakwaso na yin yunkurin kwace ragamar jam’iyyar, inda suka yi zargin cewa yana amfani da ‘ya’yan kwamitin koli na jam’iyyar wajen aikata laifuka da kuma daukar matakan da basu dace ba.
Sun kuma zargi kwamitin koli na jam’iyyar ta kasa da rusa majalisun zartarwa ta jam’iyyar ba bisa ka’ida ba a jihohi 10 na tarayyar Nigeria.
Da dumi-dumi: Tinubu ya Sauyawa Wasu Ministoci Ma’aikatu
Politics Digest ta rawaito da yake jawabi ga manema labarai a Ado-Ekiti, a jiya, mai magana da yawun kungiyar, Dada Olayinka Olabode wanda kuma shi ne shugaban NNPP na jihar Ekiti, ya ce an dauki matakin shari’a kan Kwankwaso da kwamitin koli na jam’iyyar .
“Mun dauki matakin shari’a don magance wannan rashin adalcin da aka yi wa mambobi sama da 7000 da aka zaba ta hanyar masalaha a matakan mazabu da Kananan Hukumomi da Jihohi a Jihar Ekiti da kuma, zababbun jami’an wannan jam’iyya kusan 100,000 a fadin Jihohi goma da wasu biyu jihohin da aka fitar da sanarwar korarsu”. Yace
“Kotun da ke Ado Ekiti ta bada sammaci ga kwamitin koli na jam’iyyar bisa zargin karya ka’idojin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, Inda aka bukace su da su bayyana a gaban kotu a ranar 19 ga Satumba, 2023. Shari’ar tana gaban Mai Shari’a Aladejana na Babban Kotun 3 na Babban Kotun Jihar Ekiti”.
Ya kara da cewa “Wannan matakin ya sabawa sashe na 2a na kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu. Haka kuma ya karya doka ta 32. 1i, 39.0, 39.1i da 39.4 na kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu mai daraja.