Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin dukkanin wasu makarantu masu zaman kansu da ke aiki a jihar.
Majiyar Kadaura24 ta Daily Telescope ta rawaito cewa an dauki matakin ne a ranar Asabar yayin ganawa da mammalla makarantu masu zaman kansu da gwamnatin jihar kano.

Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan makarantu masu zaman kansu da na sa kai, Alhaji Baba Abubakar Umar ya bayyana cewa ana bukatar dukkan makarantu masu zaman kansu da su je domin sabunta rijistar su cikin gaggawa, saboda gwamnati zata fara bayar da sabbin satifiket ga makarantun.
Sojojin Kasar Burkina Faso Sun Dakatar Da Gidan Rediyo Sakamakon Sukar Juyin Mulkin Nijar
Baba Umar ya bayyana cewa matakin ya jaddada kudirin gwamnati na ganin cewa makarantu masu zaman kansu sun bi ka’idojin da aka gindaya na gudanar da makarantu masu zaman kansu a jihar yadda ya dace .
“Muna tunatar da masu makarantu masu zaman kansu alhakin da ya rataya a wuyansu na biyan harajin kashi 10 ga gwamnati. Wannan alƙawarin kuɗi koyaushe yana haɓaka ci gaba a fannin ilimi da tattalin arziki.” in ji shi.
Mashawarcin na musamman ya tabbatar wa duk masu ruwa da tsaki cewa zai tabbatar da Adalci wajen kula da harkokin makarantu masu zaman kansu.
Ba Zamu Bari Yunkurin Juyin Mulki yayi Nasara a Nigeria ba – Rundunar Soji
Mai ba da shawara na musamman ya kuma tabbatar wa iyayen dalibai cewa zasu cigaba da basu fifikon wajen kiyaye muradun su da na ‘ya’yansu.
Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar masu makarantu masu zaman kansu reshen jihar Kano, Alhaji Muhammad Malam Adamu, ya yaba da matakin da gwamnati ta dauka, yana mai kallon matakin a matsayin abin yabawa a fannin ilimi .