Sojojin Kasar Burkina Faso Sun Dakatar Da Gidan Rediyo Sakamakon Sukar Juyin Mulkin Nijar

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Gwamnatin mulkin sojan kasar Burkina Faso ta dakatar da daya daga cikin mashahuran gidajen rediyon kasar bayan da ta yada wata hira da aka soki sabbin shugabannin sojojin juyin mulkin Nijar .

 

An dakatar da Rediyo Omega nan da nan a ranar Alhamis “har sai an samu sanarwa ta gaba,” in ji Ministan Sadarwa Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo a wata sanarwa.

Talla

Gidan rediyon wanda wani bangare ne na kungiyar yada labaran Omega mallakin dan jarida kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar Alpha Barry, ya dakatar da yada labarai bayan fitar da sanarwar da yammacin jiya Alhamis.

Yanzu-Yanzu: El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ya hakura da cikin cikin ministocin Tinubu

Tashar ta gudanar da wata tattaunawa da Ousmane Abdoul Moumouni, kakakin sabuwar kungiyar ‘yan Nijar da ke fafutukar mayar da shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar 26 ga watan Yuli ne wasu jami’an tsaron fadar shugaban kasar suka hambarar da zababben shugaban kasar ta Nijar Muhammad Bazoum.

Rikicin Aure: Ya kamata Hukumar Hisba ta shiga tsakanin G-Fresh da Sadiya Haruna – Auwal Danlarabawa

Moumouni ya yi kalaman batanci game da sabbin shugabannin Nijar,” in ji Ouedraogo, wanda kuma kakakin gwamnati ne.

Hukumar gudanarwar Rediyo Omega a ranar Juma’a ta ce za su yi duk mai yiyuwa don ganin sun koma cigaba da yada shirye-shiryensu. j

Sanarwar ta kara da cewa, umarnin ya zo ne bayan da wasu dake bayyana kansu a matsayin magoya bayan gwamnatin kasar suka fara yin barazanar zasu kai hari ga manajojin gidan rediyo da ‘yan jaridu”

Burkina Faso ta yi juyin mulkin soji sau biyu a bara, kowannen su ya haifar da wani bangare – kamar a Mali da Nijar – saboda rashin gamsuwa da gazawar da aka yi wajen dakile tada kayar bayan da yan kasar ke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...