Da dumi-dumi: Gwamnati Kano ta fara kamen Masu tallan maganin Gargajiya

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman

 

Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano, Alh. Abba El-Mustapha ya jaddda aniyar hukumar ta kawo tsafta tare da gyara a bangaren masu tallan magungunan gargajiya duba da yadda wasun su ke yada kalaman batsa da hotunan da basu dace ba da nufin tallata magungunan su dan su ja hankalin masu saya .

“A karkashin shugabancina ba zan zubawa ido wannan halayya ta yin kalaman batsa da sunan talla ta cigaba da faruwa a cikin al’umma ba, Saboda hakan ya saba da tarbiyar jihar Kano tare da koyarwar addinin Musulinci”. Abba El-Mustapha

Talla

Shugaban hukumar tace fina-finan ya bayyana hakan ne a harabar hukumar tace Fina-finan ta jihar Kano, jim kadan bayan kammala aikin kaman masu tallan maganin gargajiyar da aka samu da laifin sabawa dokar hukumar a wani aikin hadin gwiwa data gudanar tsakanin jami’an yan sanda da ma’aikatan hukumar tace Fina-finan ta Jahar Kano.

Dogaro da kai: Falakin Shinkafi ya ɗauki nauyin koyawa Daliban makarantar Shekara 230 Sana’i

A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar tace fina-fina Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, yace Alh. El-Mustapha yace doka ce tabawa hukumar damar gudanar da wannan aiki a don haka hukumar zata yiwa dokar biyayya sau da kafa domin cimma nasarar da tasa a gaba.

Idab za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a makonni biyu da suka gabata, hukumar ta soke lasisin gudanar da aiki ga dukkannin abokan huldar ta, sannan tace har sai ta tantance su tare da basu damar cigaba da aiki ciki ko har da Kungiyar masu tallan maganin gargajiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...