Dogaro da kai: Falakin Shinkafi ya ɗauki nauyin koyawa Daliban makarantar Shekara 230 Sana’o’i

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

A kokarinsa na cigaba da baiwa mata kwarin gwiwar gudanar da sana’o’i don su dogara da kawunansu, Amb. Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya ɗauki nauyin koyawa mata kimanin 230 sana’o’i daban-daban.

 

Matan wadanda ɗalibai ne na makarantar sakandire ta shekara dake Kano, sun koyi sana’o’i daban-daban don wadanda zasu iya yi a gida don su dogara da kawunansu ko da bayan sun kammala karatunsu.

Talla

Da yake zantawa da Jaridar Kadaura24, Amb. Dr. Yunusa Yusuf yace ya zabi a wannan karon ya ɗauki nauyin koyawa mata sana’o’in ne saboda muhimmancin da suke da shi a cikin al’umma da kuma yadda zasu amfanar da jama’a da dama idan sun tsaya da kafafuwansu.

Sarki Sanusi ya yi wa Tinubu karin haske, bayan ganawa da shugaban mulkin soji na Nijar

” Wadannan dalibai matan da kake ganin idan Allah ya taimakemu suka Maida hankali akan sana’o’in da aka koya musu, zaka yi mamakin yawan adadin mutanen da zasu amfana da sanar , don haka a wannan karon muka ce su zamu koyawa sana’o’in”. Inji Falakin Shinkafi

Yace a baya sun koya mata da dama sana’o’i kuma sun ga yadda suka sanar ta taimakesu wajen sauya musu rayuwa da Kuma yadda suka bunkasa tattalin arzikin yankin da suke, yace hakan ce tasa a wannan karon ma aka Kara adadin yawan matan zuwa 230.

Juyin Mulkin Nijar: Muhammad Bazoum ya bayyana halin da ya shiga a hannun sojojin Nijar

” Ina fatan yadda muka tsaya tsayin da kuka koyi sana’o’in nan ba za ku bamu Kunya ba, zaka dage ku rike sana’o’in hannu bibiyu don ku amfana ku amfanar da jama’a”. A cewar Falakin Shinkafi

Ya kuma yabawa malaman makarantar musamman Sshugabar makarantar bisa yadda suka tsaya tsayin daka wajen ganin daliban sun koyi sana’o’in wanda zai taimake su wajen dogara da kawunansu ko da bayan sun yi aure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya tura Shettima a ɓoye ya ziyarci Buhari a asibiti a London – Rahoto

Shugaban Nigeria Bola Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima,...

Gamayyar wasu kungiyoyi sun bukaci Kotun kolin Nigeria ta gaggauta yanke hukunci kan rikicin Masarautar kano

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gamayyar kungiyar masu fashin baki da...

Gwamnan Kano Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Fadar gwamnati

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince...

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...