Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gamayyar kungiyar masu fashin baki da da rajin kare Dimokaradiyya da tabbatar da shugabanci Nagari ta bukaci Kotun kolin Nigeria da ta gaggauta yanke hukunci kan dambarwar Masarautar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban Gamayyar kungiyoyin Com. Al-amin Albarrah da sakataren kungiyar Malam Saminu Habubakar suka sanyawa hannu kuma suka aikowa Kadaura24.
Sanarwar ta al’ummar jihar Kano sun damu matuka da yadda aka Sami jan kafa sama da shekara guda wajen yanke hukunci kan dambarwar wanene sahihin Sarkin Kano.

” Mu Gamayyar kungiyoyin masu fashin baki da kare Dimokaradiyya da tabbatar da shugabanci Nagari, mun damu matuka da yadda hadarin da ke tattare da rashin yanke hukunci, da kuma yadda wasu mara kishi suke kokarin yin amfani da hakan wajen kawo cikas a shari’ar, wanda hakan zai iya haifar da rashin zaman lafiya a jihar”.
Gwamnan Kano Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Fadar gwamnati
Sanarwar ta kara da cewa ” Muna kira ga alkalan Kotun kolin Nigeria da ku yi amfani da damarku wajen kawo karshen turkaturkar Masarautar Kano, domin yin haka shi ne zai tabbatar da samuwar Masarautun gargajiya a Wannan tsarin na Dimokaradiyya.
Gamayyar Kungiyoyin sun bukaci al’ummar jihar Kano da su kau da duk wasu banbace-banbance su cigaba da zama da juna lafiya .