Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS.
“Za mu dauki demokradiyya da mahimmanci, Dimokuradiyya tana da matukar wahala amma ita ce mafi kyawun tsarin gwamnati,” in ji Tinubu .

Tinubu ya gaji Umaro Embalo na Guinea Bissau a matsayin shugaban kungiyar ta ECOWAS.
Hukumar DSS ta bayyana dalilin da yasa ta gayyaci Abdul’aziz Yari
An sanar da nasar Tinubu ne a taro kungiyar karo na 63 na shugabannin gwamnatocin kasashen ECOWAS.
Taron na kungiyar ECOWAS karo na 63 shi ne taro na farko da shugaban kasa Tinubu ya halarta a nahiyar Afirka tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.