Hukumar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya wato DSS ta tabbatar da gayyatar tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari zuwa ofishinta.
Sai dai hukumar ba ta faɗi dalilin da ya sa ta gayyace shi ba, tana mai musanta “jita-jitar” da ake yaɗawa cewa an tsare shi ne saboda ya ƙi amsa wayar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Nada Haj. Amina HOD a matsayin kwamishina zai sake fito da kimar K/h Nasarawa – Matawallen Gwagwarwa
A ranar Asabar ne wasu rahotanni da aka wallafa a shafukan intanet suka ce DSS ta kama tsohon gwamnan ne saboda ya ƙi sauraron shugaban ƙasar game da zaɓen shugaban Majalisar Dattawa da aka yi a watan da ya gabata.

BBC Hausa ta rawaito DSS ta bayyana labarin a matsayin “na ƙarya” kuma “abin dariya”.
“Abu ne maras amfani ko kuma na dariya….Wannan shi ake kira shashanci a rahoto. Yari ya san dalilin da ya sa aka gayyace shi,” a cewar sanarwar da DSS ta wallafa a shafinta na Twitter.