Daga Abdulbaki Ali Sharifai
Kungiyar Kebbi Dala Farmers, ta tallafawa manoman da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya da kayan noma da wayoyin hannu da za su yi amfani dasu domin kara samun ilimi a bangaren aikin noma.
Kungiyar ta Dala Kebbi Farmers dake da rassa a jihohi 17 na Arewacin Najeriya, nada manufar ingantawa da saukakawa manoma samun kayan aikin gona kamar iri da takin zamani acikin farashi mai sauki.

Acewar shugaban kungiyar Comrade Habib S Umar, an samar da kungiyar ne domin saukakawa manoma,” an samar da wannan kungiya domin baiwa manoma horo da kuma samar musu da kayan noma cikin farashi mai sauki” inji Comrade Habib.
Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Zama Shugaban ECOWAS
Comrade Habib yacigaba da cewa” Muna basu damar ajiye kayan amfanin gonarsu har lokacin da kayan noman zasuyi darajar da zasu maida abinda suka kashe”.
“Kuma idan mun basu bashi suna biyanmu ne da kayan noma, ragowar kuma sunada damar siyar mana ko su saidawa wasu, ko kuma mu ajiye musu” Comrade Habib S Umar.
Kungiyar dai tayi hadin gwiwa ne da Kamfanin Kingo Mobile domin baiwa manoman bashin wayar hannu cikin farashi mai sauki.