Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Hukumar kula da aikin hajji ta Nigeria NAHCON, ta bayyana cewa zata fara aikin jigilar mayar da alhazan kasar gida daga kasar Saudiyya a ranar talata 04vga watan yuli 2023.
Shugaban dake kula da sashin harkokin jiragen sama na hukumar, Alhaji Goni Sanda ne ya bayyana hakan, yayin wani taro da hukumar ta gudanar a garin Makka na kasar Saudiyya.

Ya ce tsarin wanda ya fara zuwa shi zai fara dawo wa, shi za’a yi amfani da shi wajen jigilar alhazan zuwa Najeriya.
Sallah: Gwamnan Kano ya nemi afuwar Sarkin Gaya kan abun da ya faru a gidan gwamnati yau
Gwani Sanda ya kara da cewa, mahukuntan Saudiyya sun yi tsarin cewa a cikin makonni biyun farko jiragen ba za su yi aiki sosai ba, saboda yawan zirga-zirgar jiragen sama dake kwashe alhazan su zuwa kasashe daban-daban, sannan kuma da kasancewar kusan dukkan jirage za su tashi ne daga filin jirgin sama guda daya, na Sarki Abdulaziz, dake Jeddah.
Ya bayyana cewa a cikin makonni biyun farko na fara jigilar maniyyatan, jirgin kamfanin Flynas zai yi amfani da jiragen guda hudu ne kawai daga cikin su shida, domin gudanar da aikin, inda ya kara da cewa sauran biyun ana bincike akan su domin basu kulawar da ta dace .
Har ila yau, kwamishinan ayyuka na NAHCON, Alhaji Abdullahi Hardawa, ya ce hukumar ta kudiri aniyar tabbatar da cewa maniyyatan sun yi cikkakiyar biyayya ga manufofinta na jigilar kaya yayin mayar da su Najeriya.
Ya yi tir da halin wasu alhazai musamman mata da ke zuwa filin jirgin sama dauke da jakunkuna da yawa duk da sunan kayan hannu, yana mai gargadin cewa a wannan karon ba za a amince da lamarin ba.
Don haka ya yi kira ga jami’an hukumomin alhazai na jihohi da su sanar da alhazansu manufofi da tsare-tsaren don gujewa duk wata matsala da bata lokaci a filin jirgin.
“Kamfanonin jiragen sun koka matuka game da wannan hali na wasu alhazai, wanda ke jefa rayukan sauran fasinjojin da ke cikin jirgin cikin hadari. Wannan karon ba mu bari ba kamar yadda aka saba ba.
“Kuma saboda tsoron rasa wasu kayayyaki masu mahimmanci a filin jirgin sama, ya kamata mahajjata su bi ka’idojin jigilar kaya a jakunkuna da aka basu masu daukar kayan da basu wuce nauyin 32kg ba.”