Daga Aisha Aliyu Umar
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa ya kafa wani kwamiti mai mutane 5 don shirin sake bude makarantun kwana da aka rufe a jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa a aiyukan da aka dorawa kwamitin ya zama dole yayi duba da muhimmancin da makarantu ke da shi a tsarin ilimin jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi ta jihar kano Aliyu Yusuf, ya aikowa kadaura24.
Sallah: Gwamnan Kano ya nemi afuwar Sarkin Gaya kan abun da ya faru a gidan gwamnati yau
Ya kara da cewa, za a binciki dalilin rufe wadannan makarantu da gwamnatin da ta shude ta yi da nufin gano hakikanin dalilan da suka sa aka dauki matakin, wanda ake dangantawa da matsalar tsaro.
Kwamishinan ya ce a cikin wasu abubuwa kwamitin zai fito da hujjoji kan dalilin da ya sa aka rufe makarantun a daidai lokacin da ake bukatar karin irinsu domin daukar daliban jihar.
NAHCON ta ayyana ranar da za’a fara dawo da Alhazan Nigeria gida
Ya kuma bayyana cewa, kwamitin zai kai rahoto ga ma’aikatar ilimi kan halin da makarantun suke ciki da yadda za’a farfado da su musamman ta fuskar kayan more rayuwa da sauran kayan aiki a makarantar.
Hon. Doguwa ya bukaci ‘yan kwamitin a lokacin da aka kaddamar da su da su yi aiki tukuru domin ganin an cimma manufar sake bude makarantun.
Ya jaddada cewa sabuwar gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ta dukufa wajen ganin an ceto fannin ilimi.