Kwamishinan Ilimin Jihar Kano ya Bada tabbacin farfado da Ilimi a jahar

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Kwamishinan ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa ya jaddada Shirin sa na tabbatar da kudurin Gwamnatin Jihar domin farfado da darajar Ilimi.

 

Yayi wannan kalami ne a yayin ganawar sa ta farko da manyan ma’aikatan ma’aikatar tare da mukaddasan shugabannin Sassa dake karkashin ma’aikatar a ofishin sa.

Abba Gida-gida ya dakatar da albashin ma’aikata dubu 10 gwamnatin Ganduje ta dauka aiki

Kwamishinan ya ce Babban burin sa shine yaga cewa ya taimaka wajen dawo da daraja da martabar Ilimi a jihar Kano wanda ya sami tasgaro mai yawa a shekarun da suka gabata.

Tallah

Ya Kara da cewa makasudin ganawar sa da Ma’aikatan shine domin su san juna, sannan Kuma su yi masa bayani akan yadda ayyukan su suke domin samun makamar tafiyar da nasa aikin.

 

Kwamishinan ya tabbatar wa da Ma’aikatan cewa shi mutum ne wanda yake son aiki da mutane masu kwazo da rikon amana wajen gudanar da ayyukan su.

Tallah

Hon.Doguwa yace a zaman da zai yi na aiki a wannan ma’aikatar bashi da burin ya musgunawa kowa, burin sa kawai yaga kowa Yana aikin sa yadda yakamata.

” Amma Ina mai tabbatar muku da cewa duk wanda bazai bani hadin Kai muyi aiki ba to tabbas zan sa ayi waje dashi na sami chanjin sa domin aikin mu yayi kyau mu samu mu kyautata harkar Ilimi a Jihar Kano” in ji kwamishina Haruna Doguwa.

Kwamishinan wanda ya yaba da yadda yagan fasalin Ma’aikatan, yace idan suka zama masu Kara jajircewa to babu shakka bukatar sa zata biya wajen gudanar da aikin da’aka dora Masa alhakin aiwatar wa.

Daga karshe ya bayyana cewa zai yi aiki da kofofin ofishin sa a bude domin basu dama su bijiro da dabarun aiki iriiri don bunkasa ilimi a jahar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...