Daga Hafsat Abdullahi
Tsohon dan takarar gwamnan jihar kano a tutar jam’iyyar PDP Alhaji Sadiq Wali ya bukaci al’umma da su zamu masu sadaukar da kai da kuma taimakawa juna a wannan lokaci na bukukuwan Sallah babba.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da dan takarar gwamnan ya sanyawa hannu da kansa, kuma aka aikowa kadaura24.

“Duk da cewa a zaben gwamna na 2023, jam’iyyar PDP bata sami sakamako mai kyau ba, amma duk da haka ina matukar godiya da goyon baya da amana da al’ummar jihar Kano suka ba ni, yadda kuka nuna min kauna da kyautata zaton ku a gare ni, ya karamin kaimi wajen sake jajircewa don yin aiki don ci gaban jihar ta kano”. Inji Sadiq Wali
Bani da lokacin batawa wajen ramuwar gayya – Muhuyi Magaji Rimin Gado
Tsohon dan takarar gwamnan yace a lokaci irin wannan na bikin Sallah, akwai bukatar mutune musamman mawadata da su tallafawa mabukata domin su sami farin ciki a ransu, “hakki ne da ya rataya a wuyanmu mu tallafawa masu karamin karfi a cikin al’ummarmu”.

“Sannan ina kira ga daukacin mazauna jihar Kano da su rungumi dabi’ar hadin kai da zaman lafiya, mu ajiye banbance-banbancen siyasa a gefe, mu taru domin ci gaban jiharmu, ta hanyar tattaunawa, fahimtar juna da mutunta juna, idan mukai hakan zai taimaka mana wajen samarwa kano makoma ta gari”. A cewar Sadiq Wali
“Ina kara tabbatar wa al’ummar Jihar Kano cewa, duk da yadda sakamakon zabe ya fito, amma na ci gaba da dagewa wajen kyautata rayuwar al’ummarmu. Zan ci gaba da ba da shawarar samar da shugabanci nagari, da rikon amana, da aiwatar da manufofin da zasu zama masu muhimmanci ga bukatun jama’armu, kuma za mu iya yin aiki tare don ganin Jihar Kano ta ci gaba ta kowacce fuska”. Inji shi
Sadiq Wali ya kara da cewa “A wannan lokaci na farin ciki, ina mika sakon gaisuwata ga al’ummar musulmi da daukacin mazauna jihar Kano, ina fatan wannan Sallah zata kawo farin ciki, kwanciyar hankali, da albarka a rayuwarku. Ina fata za mu hada kai domin gina jihar Kano”.