Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da biyan albashin ma’aikata 10,000 wadanda gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta dauka aiki, har sai an gudanar da bincike.
Akanta Janar na jihar Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano .

Abdulsalam ya ce ma’aikatan da abin ya shafa sun yi aiki ne a ƙarshen gwamnatin da ta gabata.
Cutar Zazzabin Maleria ta bulla a kasar Amuruka
Ya ce an kafa wani kwamiti da zai binciki yadda aka dauke su aiki a ma’aikatun gwamnati, inda ya tabbatar da cewa sakamakon bincike ne zai sa asan makomarsu wadanda abun ya shafa.

Akanta Janar din ya kuma sanar da dakatar da sauya wuraren aikin da gwamnatin da ta gabata ta yi wa wasu ma’aikatan, Inda ta bukaci kowa ya koma Inda yake tun da farko.
Abdulsalam ya bayyana shirin sabuwar gwamnati na biyan albashin ma’aikata a ranar 25 a kowane wata, domin ya bayyana cewa za a biya ma’aikatan da suka yi ritaya hakkokin yadda ya kamata.
Ya kuma bayyana cewa sabuwar gwamnatin za ta yi aiki da asusu guda domin magance zurarewar kudaden gwamnati .