Mahukunta harkokin lafiya a Amurka sun ce a karon farko cikin shekaru 20, cutar malariya ta bulla a kasar.
An ba da sanarwar ce bayan gano mutun hudu dauke da ke ita a Florida watanni biyu da suka gabata,

Jami’an gwamnatin jihar Florida sun fitar da gargadi tare da jan hankalin mazauna yankin su rinka tsaftar muhallinsu da amfani da gidan sauro da maganin feshi.
Hajjin bana: Yadda Alhazan Najeriya Dubu 10 Suka Rasa Tantuna A filin Mina dake Saudiyya
Haka kuma an fitar da irin wannan gargadi a jihar Texas.

Ana iya cewa babu zazzaɓin maleriya a Amurka ko ba kasafai ake samunta ba a kasar, akasari mutane ne ke shiga, amma masana kimiyya sun yi gargadi cewa a yanzu zazzabin na iya yaduwa saboda sauyin yanayi.
Maleriya na haddasa zazzabi mai tsanani da kasala. Kuma tana sanadin rayukan dubban mutane a duk shekara a fadin duniya.