Cire tallafin Mai da na yi, baya cikin jawabina na ranar rantsuwa

Date:

 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce shi da kansa ya zaɓi ya bayyana cire tallafin man fetur a ranar farko da ya zama shugaban ƙasa duk da cewa ba a rubuta shi ba a cikin jawabin da ya gabatar.

 

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da ‘yan Najeriya mazauna Faransa ranar Juma’a, kamar yadda mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman Dele Alake ya faɗa cikin wata sanarwa.

 

Sanarwar ta ce: “Tinubu ya yi bayani cewa mai ba shi shawara kan harkokin kuɗi Wale Edun, da mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman Dele Alake ba su saka maganar cire tallafi ba a jawabinsa, amma ya ji cewa ya kamata ya kawo ƙarshensa a ranar farko.”

 

Shugaban ya kuma bayyana tallafin a matsayin “zamba” da ke “hana cigaba” yayin ganawar tasa da ‘yan Najeriya.

 

Tun daga ranar 29 ga watan Mayu da Tinubu ya sanar da cewa “tallafin man fetur ya tafi” farashin man ya ninninka, inda ake sayar da lita ɗaya kan N540 zuwa sama saɓanin N195 da aka saba sayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...