Cire tallafin Mai da na yi, baya cikin jawabina na ranar rantsuwa

Date:

 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce shi da kansa ya zaΙ“i ya bayyana cire tallafin man fetur a ranar farko da ya zama shugaban Ζ™asa duk da cewa ba a rubuta shi ba a cikin jawabin da ya gabatar.

 

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da ‘yan Najeriya mazauna Faransa ranar Juma’a, kamar yadda mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman Dele Alake ya faΙ—a cikin wata sanarwa.

 

Sanarwar ta ce: “Tinubu ya yi bayani cewa mai ba shi shawara kan harkokin kuΙ—i Wale Edun, da mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman Dele Alake ba su saka maganar cire tallafi ba a jawabinsa, amma ya ji cewa ya kamata ya kawo Ζ™arshensa a ranar farko.”

 

Shugaban ya kuma bayyana tallafin a matsayin “zamba” da ke “hana cigaba” yayin ganawar tasa da ‘yan Najeriya.

 

Tun daga ranar 29 ga watan Mayu da Tinubu ya sanar da cewa “tallafin man fetur ya tafi” farashin man ya ninninka, inda ake sayar da lita Ι—aya kan N540 zuwa sama saΙ“anin N195 da aka saba sayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related