Ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje a Abuja

Date:

 

Ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje da dama a fitaccen rukunin gidaje na Trademore Estate dake Lugbe a babban birnin tarayya Abuja.

 

Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta bayyanawa manema labarai cewa, ambaliyar ruwan ta tafi da direban wata mota kirar Peugeot 406 a kan titin Imo dake cikin rukinin gidajen, yayin da aka ceto wasu mutane 4 wadanda aka tabbatar cewa suna cikin koshin lafiya.

Binciken bidiyon Dala: Ganduje ya mayarwa Muhuyi Magaji Martani

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ambaliyar ta lalata kadarori na miliyoyin naira sakamakon ruwan sama da aka yi a safiyar ranar Juma’a.

Sabon Babban Sufeton yan sandan Nigeria ya kaddamar manufofinsa

An ga mazauna yankin a lokacin da ake ruwan, suna kokarin ceton rayukansu da dukiyoyinsu bayan da ruwan ya mamaye masu gidaje.

Rukunin gidajen Trademore ya shafe shekaru yana fama da munanan matsaloli na ambaliya wanda ya haddasa rashin rayuka da kuma asarar dukiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...