Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Ibrahim Garba Shu’aibu a matsayin babban Sakataren yada labaran mataimakin gwamna Kwamarat Aminu Abdulssam.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
Kadan ya rage da na nada Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano – Kwankwaso
Ibrahim Shu’aibu yayi digirinsa a jami’ar Bayero dake Kano, Kuma kafin nadin na shi shi ne wakilin jaridar Thisday a kano Kuma shi ne shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai dake aiki a Kano.
Sauran wadanda aka nada sun haɗar da
2. Lawan Adamu Miko, Senior Special Assistant, Protocol
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden mukamai
3. Abubakar Tijjani Kura, Senior Special Assistant, Administration
4. Muhammad Garba Gwarzo, Senior Special Assistant, Political Matters
5. Abubakar Salisu Mijinyawa, Special Assistant, Domestic
6. Usman Nura Getso, Personal Assistant, Administration
7. Hamza Ahmad Telan Mata, Personal Assistant, Photography
Sanarwar ta ce dukkanin nade-naden sun fara aiki ne nan take