Maniyyatan Kano 156 ba za su je aikin hajjin bana ba – Lamin Rabi’u

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kano ta ce akalla maniyyatan jihar 156 ne za su rasa aikin hajjin bana.

Hakan ya faru ne sakamakon sayar da kujeru fiye da yadda aka ƙayyade da tsoffin jami’an hukumar da gwamnatin jihar ta dakatar suka yi.

Kadan ya rage da na nada Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano – Kwankwaso

Lamin Rabi’u ya bayyana cewa za a binciki jami’an da suka aikata wannan laifi tare da gurfanar da su a gaban kotu, bayan kammala aikin Hajji bana.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden mukamai

A lokacin da yake zantawa da manema labarai, Darakta Janar na hukumar, Laminu Rabiu ya ce hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ware wa Kano kujeru 6,144, amma jami’anta sun sayar da ƙarin kujeru 156.

Daraktan ya kuma yin kira ga waɗanda abin ya shafa da su yi haƙuri, tare da alƙawarta musu cewa za a sanya su a cikin sahun farko a aikin Hajji mai zuwa.

Ya zuwa yanzu Hukumar jin Daɗin Alhazan ta Kano, ta yi jigilar maniyyata 2,558, zuwa ƙasa mai tsarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...