Wani Mutum ya mayar da littafin da ya ara bayan shekaru 65

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Wani mutum ya mayar da wani littafin almara game da wata ƙasar kwatance mai taken George Orwell’s 1984, zuwa ɗakin karatun Amurka da ke jihar Oregon bayan shekara 65.

 

A wani saƙo da ya rubuta kuma ya cusa a cikin littafin, mutumin mai shekara 86 wanda ya bayyana sunansa da WP kawai ya ce kamata ya yi ya mayar da littafin zuwa ɗakin karatu na Mulnomah da ke Portland saboda fa’idar da yake shi har a zamanin yau.

Kadan ya rage da na nada Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano – Kwankwaso

“Bayan sake-karantawa karo da dama, na fahimci cewa, fiye da kowanne lokaci a baya, kamata ya yi a sake buga wannan littafi don samun sa a cikin jama’a,” rubutun ya ce.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden mukamai

Labarin almarar ya yi nuni ne da taken da ya shafi mulkin kama-karya da kuma tsage gaskiya.

“Ya kamata na mayar da wannan littafi ne a 1958, lokacin da nake shirin kammala karatu a [Jami’ar Jiha ta Portland], amma ban samu damar yin hakan ba,” ya rubuta a cikin saƙon.

“A yi min afuwa kan wannan dogon jinkiri. A shekara 86, ina so a ƙarshe na cire tunanin daga zuciyata,” in ji shi.

Mutumin ya ce a duk lokacin da ya sake karanta wani ɓangare na littafi, sai ya ji ya sake motsa masa kwaɗayin ya mayar da shi ɗakin karatun da ya ara.

“Muhimman sassan littafin har yanzu suna da tasiri kamar yadda suke da shi shekara 65 da ta wuce,” a cewarsa, inda takanas ya nunar da wani sashe a cikin shafi na 207. “A taƙaice ku ƙara kalmomin intanet da shafukan sada zumunta, za ku ji tamkar kuna karanta wani game da shekara ta 2023,” ya ce.

Littafin almarar wanda aka wallafa a 1949, an tsara shi ne a wata duniya inda gwamnatin kama-karya take murƙushe tunanin tsage gaskiya.

Kasuwar littafin ta buɗe a Amurka cikin 2017 jim kaɗan bayan wani babban mai ba da shawara ga Donald Trump, wanda shi ne shugaban ƙasa a lokacin, ya ce fadar White House na fitar da “bayanai masu shigen gaskiya” a wani rikici game da girman taron mutanen da suka halarci bikin rantsar da shi.

Da yake mayar da martani ga littafin da aka mayar, Ɗakin Karatu na Multnomah County ya ce ba za a ci mutumin tara a kan mayarwar a makare ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...