Daga Aisha Muhammad Adam
A halin yanzu dai shugaba Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da sabon shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa, dake Abuja.
Haka kuma a ofishin shugaban kasar domin ganawa akwai gwamnan jihar Imo kuma shugaban kwamitin zaben majalisar dattawa na jam’iyyar APC, Hope Uzodinma wanda ke tare da tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje.
Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
Shi ma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu yana cikin fadar Villa.
A safiyar yau ne dai shugaba Tinubu ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ofishin sa.
Har yanzu babu cikakken bayani kan ganawar ta su.