Masarautar zazzau ta bayyana dalilin da yasa ta soke hawan Sallah Babba

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Masarautar Zazzau ta soke bikin hawan daba a bikin Babbar Salla mai zuwa.

 

Ya ce matakin ya zo ne bayan tafiyar da Mai martaba Sarkin Zazzau Mallam Ahmed Nuhu Bamalli ya yi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mallam Yusuf Abubakar Hayat, sakataren masarautar yana sanar da wannan mataki a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 12 ga watan Yuni.

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Sanarwar ta kara da cewa, Sarkin wanda tuni ya taya al’ummar masarautarsa ta Zazzau murnar barka da sallah, ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Najeriya su gudanar da addu’o’i don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

 

Ana shafe tsawon kwana uku ana hawan dawaki a Masarautar Zazzau duk shekara, a wani ɓangaren na bikin babbar salla.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...