Ku gina al’umma maimakon ku rika sace dukiyoyinsu – Kwankwaso ya fadawa ‘yan siyasa

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

 

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci ‘yan siyasa da su rika gina jama’a maimakon sace dukiyar al’ummar.

 

“Kudi ba shi ne komai ba, abun da ya fi dacewa kawai ku mai da hankali wajen inganta rayuwar al’ummar da suka zabo ku”. Inji Kwankwaso

Gobara ta tashi a Gidan da Ganduje ya Koma makonni biyu da suka gabata

Ya ba da wannan shawarar ne a Minna a ranar Alhamis, a lokacin da yayin wata lacca da aka shirya a cigaba da bukukuwan da ake gudanarwa gabanin rantsar da zababben gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago.

Idan kana son sayar da gine-ginen gwamnati ga abokanka da iyalanka, to ka bari sai ka bar ofis, lokacin ne za ka yi nadama,” inji Kwankwaso.

Zargin Kisan Kai: Ba mu da hujjojin da zasu tabbatar da zargin da ake yiwa Doguwa – Gwamnatin Kano

Tsohon gwamnan ya bukaci zababben gwamnan da ya zuba jari mai tsoka a fannin ilimi da tsaro domin amfanin jihar Neja ko kuma ya yi danasani a nan gaba, ya kara da cewa jarin da ake zubawa a fannin ilimi ba’a iya ganin shi nan take, amma a karshe zai haifar da sakamako kai kyau ga Kai da Kuma al’ummar da zaka shugabanta.

Ya kara da cewa idan Bago yana so zama gwamnan da zai taka rawar gani, to dole sai zage damtse ya fara aiki da zarar an rantsar da shi domin ci gaban al’ummar Neja da inganta tattalin arzikin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...