Zargin Kisan Kai: Ba mu da hujjojin da zasu tabbatar da zargin da ake yiwa Doguwa – Gwamnatin Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Babban lauyan jihar Kano kuma kwamishinan shari’a, Musa Abdullahi Lawan, ya wanke shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa daga zargin kisan kai.

 

Musa Lawan, wanda ya zanta da manema labarai a Kano ranar alhamis, ya ce bisa la’akari da bayanan da aka yi a baya, ma’aikatar ba za ta iya tabbatar da tuhume-tuhumen laifuffukan da suka hadar da hada baki, tada zaune tsaye, saka wuta da kuma kisan gilla ga Doguwa ba.

Gobara ta tashi a Gidan da Ganduje ya Koma makonni biyu da suka gabata

β€œBa mu iya samun isassun shaidun da za su danganta Doguwa da laifukan da aka ambata ba, la’akari da kwararan hujjojin da aka bayar a kan sa,” in ji Kwamishinan.

Ba zan baiwa ‘yan Nigeria Kunya ba – Tinubu

Ya ce iΖ™irarin waΙ—anda su ka ce laifin Doguwa ne cike ya ke da cin karo da juna kuma ba su iya samun shaidar likita da ke tabbatar da mutuwar wadanda aka kashe ba.

β€œMun dogara ne a kan bayanan binciken da β€˜yan sanda suka yi kamar yadda yake kunshe a cikin kundin bayanan lamarin da aka aiko daga FCID ba tare da jin tsoro, alfarma ko son zuciya ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related