Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gobara ta tashi a gidan da gwamnan jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje, ya koma makonni biyu da suka gabata.
Majiyar Kadaura24 SOLACEBASE Gobarar dai ta tashi ne da yammacin ranar Litinin, in da ta kone kaya na miliyoyin Naira.
Da dumi-dumi: Ganduje ya mika muhimman bayanan gwamnatin Kano ga Abba Gida-gida
Gidan Gandujen dai na nan akan titin Miagun, bayan Kano Club, a unguwar Nasarawa GRA Kano.
Akwai masu shirin tayar da hatsaniya a lokacin rantsar da sabbin gwamnatoci a Najeria – DSS
Jaridar ta ce majiya mai tushe ta shaida mata cewa, gobarar ta kone sashin da ake kiwon shanu da sauran dabbobi kuma da yawa daga cikin dabbobin sun mutu.
Da aka tuntubi babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya ce ba ya gari, don haka ba shi da masaniyar faruwar lamarin.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf, ya tabbatar da tashin gobarar.
Ya kuma ce an shawo kanta a lokacin da jami’ansu suka isa gidan.