Kungiyar yan Jaridu ta ARTV ta karrama Hadimin Ganduje Aminu Dahiru

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Kungiyar yan jaridu ta kasa reshen gidan Talabishin na Abubakar Rimi wato (NUJ ARTV Chapel) ta karrama mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje a fannin hoto, Aminu Dahiru Ahmad da lambar yabo.

 

Da yake mika lambar yabon ga Aminu Dahiru Shugaban kungiyar Kwamared Abubakar Shehu kwaru yace sun karrama mataimaki na musamman ga gwamnan ne bisa irin gudunmawar da yake baiwa matasa da kuma kungiyar.

Ku gina al’umma maimakon ku rika sace dukiyoyinsu – Kwankwaso ya fadawa ‘yan siyasa

“Mun baiwa Aminu Dahiru Ahmad wannan lambar yabo ne saboda gagarumar gudunmawar da ya ke bayarwa wajen bunkasa reshen Kungiyar mu da kuma aikin jarida a jihar Kano baki daya”. Inji Abubakar Kwaru

Hadimin Ganduje Aminu Dahiru ya baiwa wasu matasa tallafin karatu a Kano

Yace a lokuta da dama Aminu Dahiru ya kan taimakawa matasa don su dogara da kawunansu, sannan kuma yana taimakawa kungiyar irin na mu don su sami damar inganta walwalar mambobinsu .

Jim kadan bayan karbar lambar yabon Aminu Dahiru Ahmad ya godewa kungiyar bisa karramawar da suka yi masa, sannan yace hakan zai taimaka wajen karamasa kwarin gwiwar cigaba da taimakawa kungiyoyi.

” Ni matashi ne bani da wani dalili da bazan taimakawa matasa yan uwana matasa ba, shi matashi idan ka taimake shi ba shi kadai ka taimaka ba don haka muke amfani da damar da Allah ya bamu wajen taimakawa matasa daidai gwargwado.

Aminu Dahiru ya kuma bukaci kungiyoyi da su rika mai da hankali wajen samar da walwala ga mambobinsu, domin hakan shi ne ribar kungiya da Kuma taimakawa juna.

Aminu Dahiru dai ya sami lambobin yabo daga kungiyoyi daban-daban bisa yadda yake taimakawa wajen cigaba da inganta rayuwar matasa ta fannoni daban-daban

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...