Daga Rukayya Abdullahi Maida
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya sha alwashin ba zai baiwa ‘yan Najeriya kunya ba.
Tinubu ya bayyana haka ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama shi da lambar girmamawa ta kasa (GCFR) a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis.
Ya ce ya fahimci karramawar da Kuma aikin da ke gabansa, inda ya yi alkawarin ba zai baiwa shugaban kasa da ‘yan Nijeriya kunya ba.
“Ni mutum ne mai saukin kai wanda ya ci gajiyar goyon baya da fatan alkhairin al’ummar Najeriya. Jama’a sun dogara gare mu, Ka yi aikinka nima zan yi nawa don inganta rayuwar al’ummar Nigeria .
“Idan na shigo faggen dole ne na yi abun da ya dace wajen inganta fannin tsaro, tattalin arziki, noma, ayyuka, ilimi, lafiya da wutar lantarki da kuma sauran bangarori , ya mai girma Shugaban kasa da kai da yan Nigeria dole ne in yaba muku in kuma fidda ku kunya.”
Ya godewa Buhari bisa karramawar da ya yi masa da kuma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya samu kambun babban kwamandan Niger (GCON).
Ya kara da cewa sadaukarwar da Shugaban kasa ya yi na samar da kyakkyawan shugabanci ga dimokuradiyya ba abu ne mai sauƙi ba.
Tinubu ya kuma yaba wa shugaba Buhari bisa karrama marigayi MKO Abiola, wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka soke ranar 12 ga watan Yunin 1993.