Akalla kimanin mutane huɗu ne suka rasu sakamakon fashewar tukunyar iskar gas a wani shagon mai akin walda da ke karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar DSP Sanusi Abubakar ya tabbatar wa Gidan Talabijin na Channels cewa fashewar ta auku ne a ranar Lahadi.
Sai dai ya ce fashewar ba ta da nasaba da rashin tsaro da ake fama da shi a yankin, illa tukunyar gas ce kawai ta fashe.
DSP Sanusi ya ce ba ya ga mutum huɗu da suka rasu, akwai wasu mutum uku da suka jikkata kuma suna karɓar magani a asibiti.