Daga Umar Shu’aibu
Hadakar kungiyoyin Fulanin jihar Kano, sun sauke tsohon shugaban su Kamal Shu’aibu Umar biyo bayan wani zaman gaggawa da ‘yan’yan kungiyar suka yi.
Wannan na kunshe cikin wata takarda dake dauke da sunayen sabbin shugabanni da kungiyar ta fitar a baya-bayan nan.
Rahotanni na nuni da cewa cire tsohon shugaban wanda shi ne Sarkin Fulanin Masarautar Karaye, Dr. Kamal Shuaibu ne saboda gaza kawo ci gaban da ake bukata.
Hawan Nasarawa: Fulani Ku Dawo Kano da kiwo ko a daina tsangwamar ku- Ganduje
“Sarkin Fulanin Karaye ya gaza wajen saukin nauyin da muka dora masa, musamman ganin yadda Gwamnati mai tafiya ta doro kudurori na ciyar al’ummar Fulani mazauna Kano gaba.
“Wannan ya hada da samar da zaman lafiya, aiwatar da aikace-aikacen da muradan kungiya da dai sauran su.
“Bisa wannan hujjoji ne zai mika duk wani abu na shugabanci ga sabon shugaba, Dr. Hussaini Umar Ganduje,”.