Daga Aisha Aliyu Umar
Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta ce ta kama wasu mutane 72 da ake zargi da satar wayoyin hannu da bata-gari, wadanda ake kira da Kauraye, a babban birnin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), CSP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Katsina.
Isah ya ce yankunan da ‘yan sandan suka kai farmaki kuma har suka kama wadanda ake zargi sun hada da Sabuwar Unguwa, Gadar Nayalli, Modoji, Tudun YanLihida da kuma Kwabren Dorawa.
Sauran yankunan sune Janbango, Abattoir, Filin Canada, Lambun Dankwai, Kofar Marusa, Tsalawa, da Chake, da dai sauransu.
Majalisa ta 10: Yan Majalisun adawa sama da 183 sun fara yunkuri kafa Shugabancin majalisar
“Rundunar ta na mika godiyarta ga daukacin jama’ar jihar katsina bisa goyon bayan da suke baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar.
Rundunar ta umurci jama’a da su kai rahoton duk wani mutum ko wata kungiya da suke yzargi ga ‘yan sanda ta lambobin waya kamar haka: 08156977777, 09053872247.”