Majalisa ta 10: Yan Majalisun adawa sama da 183 sun fara yunkuri kafa Shugabancin majalisar

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Zababbun ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyun adawa sun kafa wani kwamiti da zai tantance tare da zabo ‘yan takarar da za su tsaya takarar shugaban majalisar wakilai ta 10.

 

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, zababbun mambobin sun bayyana Nicholas Mutu a matsayin shugaba, da kuma Victor Ogene a matsayin sakataren kwamitin mai mutane 11.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Ogene da wasu mambobin kungiyar uku, ta ce kwamitin na da mako guda ya gabatar da rahotonsa.

Majalisa ta 10: APC ta bayyana sunayen wadanda ta ke so su zama shugabannin majalisar

Mambobin, wadanda suka fito daga jam’iyyu takwas da ke kiran kansu a matsayin “Greater Minority” sun bayyana cewa suna da mambobi 183, suna da abin da ake bukata wajen samar da shugaban majalisar sabanin 173 na jam’iyyar APC .

 

“A bisa yarjejeniyar da jam’iyyun adawa mun kuduri aniyar shiga cikin zaben ta hanyar gudanar da sahihin zabin shugabanci.

 

Dangane da wannan kuduri, “Mafi rinjaye” na majalisar wakilai ta 10, sun hada da wani kwamiti mai mutum 11 – wanda shugaba da sakatare suka karawa aiki – wanda aka dorawa alhakin tantancewa da kuma ba da shawarwarin masu neman zama shugaban majalisar wakilai da kuma shawarwarin daga karshe.

 

“Tare da tsohon dan majalisar wakilai, Nicholas Mutu a matsayin shugaba, da Victor Ogene a matsayin sakatare, kwamitin yana da mako guda don gabatar da rahotonsa,” in ji su.

Mambobin kwamitin sun hada da, Abdulmumini Jibrin, mataimakin shugaban NNPP, Oluwole Oke, PDP, Gaza Jonathan Gbefwi, SDP, da Beni Lar, PDP.

Sauran sun hada da, Dr Ali Isa, PDP, Kabiru Rurum, NNPP, Donatus Mathew Kuzalio, LP, Yusuf Salisu Majigiri, PDP, Nnabuife Chinwe Clara, YPP, Maureen Chinwe APGA, Rep. Idris Salman, ADC, da Rep. Afam Ogene Secretary. LP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...