Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar kano ta tabbatar da kama wasu matasa 27 da ake zargin su da kwacen waya da kuma wasu dake siyan wayar sata.
” Mun sami wannan nasarar ne sanadiyar tsarin ‘yansandan cikin al’umma wato community policing, inda al’umma ke bamu rahotannin maboyar bata gari a wurare daban-daban a kano”. Inji Kiyawa
Hakan na kunshe cikin wani sakon murya da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikewa manema labarai a kano.
Majalisa ta 10: Yan Majalisun adawa sama da 183 sun fara yunkuri kafa Shugabancin majalisar
SP Kiyawa ya ce ba za su ragawa dukkan wanda aka kama da laifin kwacce waya a kano ba, ya kuma bukaci al’umma su ci gaba da sanya ido kan yadda abubuwa ke gudana a unguwannin su domin dakile dukkan bata garin da suke aikata barna.
Matsalar kwacen waya dai ta dade tana ci wa al’ummar jihar kano tuwo a kwarya, inda al’umma da dama suka jikkata har ma a wasu lokutan wasu suka rasa rayukan su duk a sanadiyya kwacen waya a kano.