‘Yan sanda sun kama mutane 72 da ake zargi da kwacen wayar salula a Katsina

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta ce ta kama wasu mutane 72 da ake zargi da satar wayoyin hannu da bata-gari, wadanda ake kira da Kauraye, a babban birnin jihar.

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), CSP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Katsina.

 

Isah ya ce yankunan da ‘yan sandan suka kai farmaki kuma har suka kama wadanda ake zargi sun hada da Sabuwar Unguwa, Gadar Nayalli, Modoji, Tudun YanLihida da kuma Kwabren Dorawa.

DA DUMI DUMI: Kotun Sauraren Kararrakin Zaɓe ta ɗage Shari’ar da ake Kalubalentar Tinubu Zuwa Alhamis

Sauran yankunan sune Janbango, Abattoir, Filin Canada, Lambun Dankwai, Kofar Marusa, Tsalawa, da Chake, da dai sauransu.

Majalisa ta 10: Yan Majalisun adawa sama da 183 sun fara yunkuri kafa Shugabancin majalisar

“Rundunar ta na mika godiyarta ga daukacin jama’ar jihar katsina bisa goyon bayan da suke baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar.

Rundunar ta umurci jama’a da su kai rahoton duk wani mutum ko wata kungiya da suke yzargi ga ‘yan sanda ta lambobin waya kamar haka: 08156977777, 09053872247.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...