Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya taya al’ummar musulmin jihar kano da ma Najeriya murnar zagayowar wannan lokaci na Sallah tare da addu’ar Allah ya karɓi duk addu’o’i da ibadun da aka gudanar a watan Ramadana.
Ya bukace al’umma su yi koyi da darussan da suka koya a watan Ramadan na sadaka, ibadu, soyayya da zaman lafiya a rayuwarsu ta yau da kullum.
Sallah: NUJ reshen Kano ta bukaci zababbun shugabannin su magance kalubalen da kasar nan ke fuskanta
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24.
Abba Gida-gida ya Gargaɗi al’umma game da tukin ganganci, yayin bukukuwan Sallah
A cewarsa…”Ramadan wata ne mai falala mara iyaka, kyauta da lada ga musulmi, wannan lokaci ne na sadaukar da kai wajen yin addu’a da kyautata alaka da Allah (S.W.T).”
Don haka Gawuna ya yi kira ga al’ummar jihar kano da su ci gaba da dagewa wajen yin addu’o’in samun hadin kai, zaman lafiya da ci gaban Kano da Nijeriya baki daya.
Ya kuma godewa al’ummar jihar kano bisa goyon bayan da suke ci gaba da baiwa Gwamnatin Jiha, Inda ya yi fatan zasu Kara dagewa wajen cigaban da yin addu’o’in samun zaman lafiya da karuwar arziki.