Daga Sani Idris Maiwaya
Zababben Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf yace zai yi Sallar Idin karamar Sallah ne tare da jagoran Jam’iyyar NNPP na kasa Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso a Masallacin marigayi Alhaji Musa Sale Kwankwaso, dake Miller Road, Kano.
Babban Sakataren yada labaran zaɓaɓɓen gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24.
Rarara ya Magantu kan korar yan sandan dake bashi kariya
Sanarwar tace za’a tada Sallah Idin ne da misalin karfe 8:00 na safe.
“Duk wakilan kafafen yada labarai da ke son Shaidar yadda Sallar Idin zata kasance suna da damar hallara a masallacin da karfe 7:30 na safe”. A cewar sanarwar