Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR JP CNOL ya bayyana ganin jaririn watan Shawwal a yau alhamis 29 ga watan Ramadan shekara ta 1444 Miladiyya.
A wani zama da Mai martaba Sarkin ya gudanar da yan Majalisar sa da sauran Malamai, bayan tattaunawa akan ganin Jinjirin watan Shawwal yace sun sami umarni daga Mai Alfarma Sarkin musulmi na ganin watan Shawwal Wanda gobe Juma’a shine 1 ga watan shawwal 1444 bayan hijira.
Yanzu-Yanzu: An ga watan karamar Sallah a Saudiyya
Alhaji Aminu Ado Bayero yace an samu ganin jaririn watan Shawwal din ne a Borno, Katsina, Jigawa, da Kasar Saudia Arabia
Da dumi-dumi: Sarkin Musulmi ya tabbatar da ganin watan Sallah a Nigeria
A don haka Mai Martaba Sarkin Kano yayi umarnin alumar musulmi su sauke azumin Ramadan kuma gobe juma’a su tashi da shirin fita sallar idin Karamar Sallah.
Sanarwar da Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24 yace Sarkin Kano ya bukaci al’ummar musulmi su yi dukkan bukukuwan sallah lafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya karbi ibadun da mukayi a watan na Ramadan yasa muna daga cikin bayinsa da ya “yantar a cikin watan.
Daganan Mai martaba Sarkin Kano yayi umarnin fitar da zakkar fidda kai ga duk wanda Allah ya horewa.