Daga Aisha Aliyu Umar
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad III ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.
Yanzu-Yanzu: An ga watan karamar Sallah a Saudiyya
Sarkin Musulmin ya ce ganin jinjirin watan da aka yi a a kasar ya sanya ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1444.
Rarara ya Magantu kan korar yan sandan dake bashi kariya
Kwamitin tantance ganin wata karkashin jagorancin Maigirma Wazirin Sakkwato Farfesa. Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan a bana.
Akasarin Musulmai a fadin duniya dai sun tashi da Azumin watan Ramadan ranar 23 ga watan Maris 2023.
Saudiyya tuni ta sanar da ganin watan a garin garin Tumair wanda hakan ke nufin ranar Juma’a ne sallah. Ko da yake da farko sai da ta ba da sanarwar ba a ga watan ba a lardun gashin ƙasar.
A Iran kwamitin ganin watan ƙarƙashin jagorancin shugaban addini na ƙasar Ali Kamenei ya ce ba a ga watan ba, don haka sallah sai ranar Asabar.