Sallah: Hadimin Ganduje Aminu Dahiru ya tallafawa shugabannin jam’iyyar APC na Gwale

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

 

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan kano akan harkokin hotuna wato SSA Photography Aminu Dahiru Ahmad ya raba kayan abinchi ga shugabannin jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale da wasu daga cikin matasa da suke baiwa jam’iyya gudummawa.

 

” Mun raba wadannan kayane saboda mu ma mudan bada ta mu gudunmawa wajen ganin shugabannin wannan jam’iyya ta mu sun Sami farin ciki a wannan wata mai alfarma”. Inji SSA Photography

Yanzu-Yanzu: An ga watan karamar Sallah a Saudiyya

Yayin gudanar da rabon kayan abinchin a wannan rana ta laraba, SSA Aminu Dahiru ya yabawa da kokarin da shugabannin jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale suke yi don cigaban jam’iyyar.

Rarara ya Magantu kan korar yan sandan dake bashi kariya

” Ganin irin kokarin da kuke yi yasa Nima naga dacewa bada wannan tallafi da nake fata zai taimaka koyaye ne wajen nuna godiya ta a gareku da Kuma sanya farin ciki a zukatanku”. Inji Aminu Dahiru

 

 

Kayan da SSA Photography Aminu Dahiru ya rabawa shugabannin jam’iyyar sun hadar da shinkafa taliya da sauran kayan masarufi da Kuma kudin cefane don su gudanar da bikin Sallah karama cikin jin dadi da walwala.

 

Shugabannin jam’iyyar sun yabawa Aminu dahiru Ahmad bisa yadda yake bada gudummawa garesu da yan jam’iyya da Kuma ɗai-ɗaikun mutane, tare da yin kira ga sauran masu rike da mukamai a gwamnati da su rika yin koyi da abubuwan alkhairin da Aminu Dahiru ya ke yiwa yan jam’iyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...