Ganduje ya kore mu daga APC, mu kuma mu ka yi masa ritaya daga siyasar Kano – Abdulmumini Kofa

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

 

Zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Abdulmumin Jibril Kofa, ya ce da yawa daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Kano Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya kore su daga jam’iyyar, Inda yace su kuma sun koya masa darasi na siyasa .

 

Idan dai za a iya tunawa, lokacin da ake tunkarar zaben 2023, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da dama sun fice daga jam’iyyar zuwa NNPP.

 

Aikin titin Abuja-Kaduna-Kano ba zai kammala a gwamnatin Buhari ba- Fashola

Jam’iyyar NNPP ta doke jam’iyyar APC mai mulki a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris bayan lashe mafi yawan kujerun majalisun tarayya da na jihohi.

 

Abdulmumini kofa, ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin gidan talabijin na Channel TV mai suna ‘Politics Today’.

 

Direban jirgin sama ya yi artabu da maciji a kan kujerar zamansa a sararin samaniya

Ya ce: “Muna da dadaddiyar alaka da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso, wanda a zahiri shi ya shigar da ni siyasa.

 

“A daya bangaren kuma, ba a son mu a APC, gwamna ba ya son mu da yawa daga cikin mu APC, don haka ya yi duk abun da zai yi don ganin ya kore mu daga jam’iyyar.

 

“Shi (Ganduje) yana fada da mu, Amma a tunanin sa baza mu iya barin jam’iyyar APC ba.

 

“ Shi yasa Muka koma muka hada kanmu muka koya masa darasin siyasar rayuwarsa.

 

Kofa ya kara da cewa abun da da sukai yi ya jawowa ‘yan majalisar wakilai na APC 18, sun rasa kujerunsu ciki har da wakilai kusan shida ko bakwai da kasar nan take amfana da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...