Mun yi takaicin yadda muka rasa kujerar gwamnan kano – APC

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce babban abin bakin ciki shi ne a ce sun rasa Kano, amma yace dole laifin wasu ne yasa suka fadi zaɓe a Kano, saboda son zuciya irin tasu.

 

Ya ce, “ Kamar Kano, a ce mun rasa Kano, to amma laifin wasu ne ya sa muka fadi a Kanon.”

Iftila’i: Wani dan jarida ya tsallake Rijiya da baya a kano

 

Shugaban na APC, ya ce “ Akwai wadanda ba su yi abin da ya kamata ba, ga shi a yanzu ya sanya ‘ya’yan jam’iyar cikin wani hali saboda nasarar da jam’iyyar ba ta samu ba, bayan ga shi su sun yi duk abin da ya kamata su yi.”

 

Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce Kano tana cikin jihohin da suke bugun kirji su ce wannan tamu ce, domin duk abin da za su yi Kano na kan gaba a lissafinsu.

 

Kuɗin masaukai ya yi tashin gwauron zabi a Makkah

Ya ce, “ Saboda wasu abubuwa na son zuciya an samu a cikin wani hali domin bai kamata a ce mun rasa Kano ba, to amma duk abin da ya samu bawa da sanin Ubangiji.”

 

“Sai da muka ja dukkanin gwamnonin jam’iyyar APC a jihohin Najeriya a kan a rage son zuciya tun kafin zabe, kuma muna ganin son zuciyar ne ya ja mana rashin nasara a jiha kamar Kano,” In ji shi.

 

Shugaban APCn, ya ce yanzu jira suke duk hayaniyar zabe ta lafa don za su dauki mataki a kan duk wanda ya yi wa jam’iyyar abin da bai dace ba.

 

Sanata Abdullahi Adamu, ya ce to amma duk da rashin nasara a Kano, suna gode wa Allah da Ya ba su nasara a zaben shugaban kasa da kuma a wasu jihohin.

 

Ya ce, “ Zaben ma da ake jira za a kammala a Adamawa da Kebbi, mu ne za mu ci in Allah Ya yarda har ma mu je mu yi guda.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...