Wata kotu a kano ta bada umarnin a yanka wani Zakara

Date:

Daga Abubakar See’d Sulaiman

 

Kotun Majistiri da ke gidan Murtala a Kano ta umarci wani mutum Isyaku Shu’aibu da ke unguwar Ja’en ya yanka Zakaransa.

 

Maƙocinsa Malam Yusuf Muhammad Ja’en ne ya shigar da ƙara Kotun kan cewa Zakaran yana shiga haƙƙinsa ta hanyar hana shi barci da yawan Cara.

 

Amma koda aka karantowa wanda ake ƙara ya ce, gaskiya ne Zakaran na yawan yin Cara kuma zai yanka shi ne a bikin “Good Friday” don haka ya roƙi Kotun da ta sahale masa zuwa ranar.

 

Freedom Radio ta rawaito mai shari’a Halima Wali ta amince inda ta umarci ya killace Zakaran kuma ya yanka shi a Jumu’a mai zuwa wato ranar “Good Friday” ɗin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...