Iftila’i: Wani dan jarida ya tsallake Rijiya da baya a kano

Date:

Daga Usaini Kabiru Minjibir

 

A daren ranar Litinin da misalin karfe takwas da minti goma wani ɗan jarida ma’aikacin gidan Radio Kano kuma mamba a kungiyar ‘Yanjaridu marubuta labarin wasanni ta kasa reshen jihar Kano, mai Suna Yusuf A. Yusuf Giginyu ya gamu da wasu ɓata gari akan hanyar sa ta komawa gida daga wajen aiki, inda suka tare shi domin kwace wayar hannun sa .

 

Sai dai cikin ikon Allah -Allah ya bashi damar kwace sharbebiyar wukar hannun su, sai dai tuni sun gudu da wayarsa ta hannu Android.

 

Ciyar da Kano Gaba ne ya Kawo Abba Kabir Yusuf, ba Ɗaukar Fansa ba – Alhaji Bashir Abubakar

A dan haka Yusuf A Yusuf ke kira ga al’umma da su dinga kula sosai idan suka hango matasa su biyu a kan babur sun nufo garesu da nufin tambayar wani wuri.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a lokuta banbanta batan gari na tare mutane a wurare daban-daban don kwace musu wayoyin su na hannu, sai dai yanzu an dan sami sauki sakamakon matakan da gwamnati da jami’an tsaro suka dauka .

 

Yanzu haka dai Yusuf A. Yusuf yana nan cikin koshin lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...